SIRRIN YASIN DA DU'A'UL JAUSHANUL-KABIR

Wannan addu'ar ana yin ta domin neman biyan bukata a wajen Allah (T) kuma tana da matukar tasiri ga yadda bayanin addu'ar take kamar haka:

ALLAH a cikin Alƙur'ani an ƙira Shi da "أَرْحَمُ الرّاحِمین" sau huɗu, kuma duk sun zo ne a yayin siffanta ALLAH ɗin. Yin zikirinta bayan ka ambaci "یا" a ƙalla sau bakwai yana kaiwa ga biyan buƙata. Yawan ambatan "یا رحمان" yana sauyawa mutum hali daga mai kaushin zuciya zuwa mai taushin zuciya. Annabi Ayuba A.S ya kira ALLAH da "أَرْحَمُ الرّاحِمین" bayan ya ambaci irin halin da yake ciki na matsaloli da damuwa. Kun san yadda ya talauce, ya rasa ƴaƴa da duk wani abu da ALLAH Ya mallaka masa, amma bai bari ya rasa harshe da zuciya don ambatan Ubangijinsa ba. To duk wani mai tsananin damuwa idan ya lizimci wannan, zai samu mafita. Bayan sunan ALLAH, da siffarsa ar-Rahman (mai rahma), akwai Siffofinsa irinsu: Ya Rahim; Ya mai Jin Ƙai, Ya Karim; Ya Mai Karamci, Ya Muƙim; Ya Mai Tsayarwa (kamar tsayuwar da sama), Ya Azimu; Ya Mai Girma, Ya Ƙadimu; Ya Daɗaɗɗe, Ya Alimu; Ya Masani, Ya Halimu; Mai Haƙuri da jinkiri, Ya Hakimu; Mai Hikima. Yin Tawassuli da waɗannan sunaye da siffofin, yana sanya mutum samun kusanci da ALLAH da kuma biyan buƙata.



إرسال تعليق (0)
أحدث أقدم