HAƊIN NA MUSAMMAN DOMIN MAGANCE MATSALAR ƊAUKEWAR SHA'AWA.
Wani lokaci ma'aurata kan tsinci kansu a cikin yanayi na ɗaukewar sha'awa, hakan na faruwa ne bisa dalilai daban-daban. Akan samu wannan matsalar a bangaren Mace wato ya kasance ta fuskantar matsalar ɗaukewar sha'awa ita kaɗai ko kuma bangaren Namiji ya kasance shi ne hakan ke faruwa da shi ko duk su biyu-biyun matsalar ta faru da su.
Idan ya kasance a ɓangare guda ne wato ɓangaren Matar ita kaɗai to hakan ka iya jawo gagarumin matsala wanda idan ba tsaya an tattauna an fahimci juna ba tana iya zama matsala babba hakan abin yake Idan Namiji ne shi kaɗai abin ke faruwa da shi.
Saboda haka yana da Muhimmanci Ma'aurata su sani cewa akwai lalura na ɗaukewar sha'awa wanda ke iya faruwa ga kowane ɓangaren to yana kyau a fito ayi bayani a fahimci juna kuma a ɗauki matakin neman Magani.
MAGANIN ƊAUKEWAR SHA'AWA:
Da farko za a nemi waken suya kamar gwagwanin madar biyar (5) a soya shi zai a niƙa ya zama gari, sai a nemi Ayaban da ake soyawa Wato (Plantain banana), za a busar da shi ya zama gari sai a ɗebi kamar gwangwani biyu na garinsa sai a haɗa da garin waken suya, sai a nemi namijin goro a shima a mai da shi gari a ɗibi kamar cokali biyar a haɗa da wancan haɗaɗɗen garin a ya mutsa sosai.
YADDA AKE AMFANI DA MAGANIN:
Za a rinƙa ɗibar babban cokali guda ana sanyawa a cikin madara na ruwa ana sha,kuma za a iya shansa a cikin fura ko nono ko kuma a kunu. Sau biyu a rana.