HANYAR LALATA SIHIRIN SOYAYYA CIKIN ƊAN ƘANƘANIN LOKACI.

Kamar yadda aka sani daga cikin sihirorin da wasu ke yi akwai sihirin soyayya. Hakan kan faru ne idan Mace na son ta mallaki Mijinta sai yadda ta yi da shi, ko dai saboda yawan saɓanin da rashin zaman lafiya  dake aukuwa a tsakaninsu. Ko kuma sanadiyyar ita Matar tana da tsananin kishi saboda haka bata buƙatar  kishiya sai ta nemi mallakar Mijin domin hana shi ƙara Aure.

Har ila yau wasu mazaje kan yi wa matansu irin wannan sihirin domin su mallaki matar saboda dalili masu yawa ko dai daga cikin waɗanda muka ambata a baya, ko kuma wasu dalilan na daban. A wani lokaci Saurayi kan yi wa budurwa irin wannan sihirin domin ya mallaketa wasu kan yi da niyyar aure. Wasu kuma domin su yi ta lalata da yarinyar da suka yi wa sihirin.

Ko ma da wani dalili ne aka yi yana da muhimmanci mu san cewa Sihiri haramun Musulunci ya haramta sihiri amma ya hallata addu'a da haka yana da kyau mu ƙaurace wa duk wani abu da zai nisantar mu daga Allah Maɗaukakin Sarki.

  

Ga yadda ake ɓata irin wannan sihiri kamar haka: 

Da farko za a samu ruwa a tofa waɗannan ayoyin sau bakwai a ruwan sai a ba wanda akayi wa sihirin ya sha. Akwai yiwuwar yayi amai ko baƙi ko kore to idan yayi aman ya samu lafiya. Idan kuma bai yi amai ba sai a yi masa wannan Addu'ar a ruwa ya sha na sati uku ko fiye da haka da inzin Allah zai samu lafiya.


Ga ayoyin kamar haka: 


قَالَ مُوسَىٰ مَا جِئْتُمْ بِهِ السِّحْرُ ۖ إِنَّ اللَّهَ سَيُبْطِلُهُ ۖ إِنَّ اللَّهَ لَا يُصْلِحُ عَمَلَ الْمُفْسِدِينَ. وَيُحِقُّ اللَّهُ الْحَقَّ بِكَلِمَاتِهِ وَلَوْ كَرِهَ الْمُجْرِمُونَ.

وَأَوْحَيْنَا إِلَىٰ مُوسَىٰ أَنْ أَلْقِ عَصَاكَ ۖ فَإِذَا هِيَ تَلْقَفُ مَا يَأْفِكُونَ . 

فَوَقَعَ الْحَقُّ وَبَطَلَ مَا كَانُوا يَعْمَلُونَ . فَغُلِبُوا هُنَالِكَ وَانْقَلَبُوا صَاغِرِينَ.   وَأُلْقِيَ السَّحَرَةُ سَاجِدِينَ. قَالُوا آمَنَّا بِرَبِّ الْعَالَمِينَ .  رَبِّ مُوسَىٰ وَهَارُونَ . 

 

إِنَّمَا صَنَعُوا كَيْدُ سَاحِرٍ ۖ وَلَا يُفْلِحُ السَّاحِرُ حَيْثُ أَتَىٰ.

اللَّهُ لَا إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ الْحَيُّ الْقَيُّومُ ۚ لَا تَأْخُذُهُ سِنَةٌ وَلَا نَوْمٌ ۚ لَهُ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَمَا فِي الْأَرْضِ ۗ مَنْ ذَا الَّذِي يَشْفَعُ عِنْدَهُ إِلَّا بِإِذْنِهِ ۚ يَعْلَمُ مَا بَيْنَ أَيْدِيهِمْ وَمَا خَلْفَهُمْ ۖ وَلَا يُحِيطُونَ بِشَيْءٍ مِنْ عِلْمِهِ إِلَّا بِمَا شَاءَ ۚ وَسِعَ كُرْسِيُّهُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ ۖ وَلَا يَئُودُهُ حِفْظُهُمَا ۚ وَهُوَ الْعَلِيُّ الْعَظِيمُ.

إرسال تعليق (0)
أحدث أقدم