YADDA ZAKA LALATA SIHIRI TA HANYAR ADDU'A CIKIN ƊAN ƘANƘANIN LOKACI.
Sau da yawa wasu na fama da matsalolin da ya shafi Sihirin iri daban-daban. Misali: Sihirin rashin lafiya, Rariyan hannu (wato ko sun samu Kuɗi baya tsayawa), ko kuma Sihirin da yake da alaƙa da hassada, maita da kambu baka amma su san hanyar da za su ɓata wannan sihirin ba ta hanyar addu'a ko kuma karanta wasu daga cikin ayoyin Alqur'ani mai girma da ke da tasiri wajen lalata sihiri ba. Bisa wannan dalili ne muka ga ya dace mu kawo maku wannan fa'idar mai sauƙi wanda kowa zai iya yi kuma za a samu biyan buƙata da gaggawa da yarda Allah akan duk wadannan nau'oi'in sihirin da muka ambata da ma wanda ba mu fada ba.
Duk wanda yake fama da laluran da ke da alaƙa da Sihiri to ya jaraba wannan fa'idar da za mu yi bayani kamar haka:
Da farko za ka yi alwala sai ka yi sallar Nafila raka' a biyu a raka'an farko zaka karanta suratul Fatiha ƙafa ɗaya sai kuma ka karanta suratul falaq ƙafa (99):
(الفلق)
قُلْ أَعُوذُ بِرَبِّ الْفَلَقِ (1) مِنْ شَرِّ مَا خَلَقَ (2) وَمِنْ شَرِّ غَاسِقٍ إِذَا وَقَبَ (3) وَمِنْ شَرِّ النَّفَّاثَاتِ فِي الْعُقَدِ (4) وَمِنْ شَرِّ حَاسِدٍ إِذَا حَسَدَ (5)
Sai ka yi ruku'u da sujudu guda biyu.
A raka'a ta biyu sai a karanta suratul Fatiha ƙafa ɗaya da suratul Nasi ƙafa (99) :
(الناس)
قُلْ أَعُوذُ بِرَبِّ النَّاسِ (1) مَلِكِ النَّاسِ (2) إِلَٰهِ النَّاسِ (3) مِنْ شَرِّ الْوَسْوَاسِ الْخَنَّاسِ (4) الَّذِي يُوَسْوِسُ فِي صُدُورِ النَّاسِ (5) مِنَ
الْجِنَّةِ وَالنَّاسِ (6)
Bayan an kammala tahiya da sallama. Sai ka yi zikirin Allah Akbar 34, Alhamdulillah 33, Subhallahi 33 ayi sallatin Annabi ɗari sai a ɗaga hannu ka roƙi Allah akan ya lalata duk wani Sihiri ko ƙulli da aka yi maka .
Tambihi: Za ayi wannan sallar na tsawon kwana bakwai kuma ana buƙatar a dai-dai lokacin da aka fara to a lokacin ya kamata a sake a washegari har sati guda. Abin nufi da zai kasance an fara shi ne da ƙarfe biyu na rana ko da dare to a ƙarfe biyu ɗin nan na rana idan da rana a ka fara za a cigaba idan kuma da dare ne to a ƙarfe biyu na dare za a cigaba. Allah ya sa mu dace🌹🌹🌹
Domin neman ƙarin bayani ku tuntuɓemu ta WhatsApp: +2347062014111