SIRRIN BISMILLAH MAI KARFIN GASKE WAJEN NEMAN BIYAN BUKATA



SIRRIN BISMILLAH 

Bismillah tana da sirrorin masu yawa wanda za a iya cewa latu'addu wala tu'usa ko mu ce babu wanda yasan adadin sirrorinta sai Allah (T) da ManzonSa (s.a.a.w). 
 
Bismillah tana da falala mai yawa daga cikin falalarta, ta zo a cikin alƙur'ani sau 114 wato duk cikan saurorin alƙur'ani sun fara ne da Bismillah in banda suratul Tauba, Duk kuwa da kasancewa ba a bude suratul Tauba da ita ba amma ta sai dai maimaita a cikin suratul-Namli inda aka ambaci sunan Annabi Sulaiman Alaihi Salam wanda a ciki aka tsoratar da kafirai akan cewa lallai su yi imani da Allah. Hakan yasa suka miƙa wuya kuma suka musulunta.

Akwai hanyoyin addu'o'in neman biyan buƙatu daban-daban da ake amfani da Bismillah.

A wannan rubutun za mu kawo ɗaya da cikin amma ku na iya ziyartan YouTube channel ɗin na Al-wahda African Tv mun kawo wasu sirrukan Bismillah masu yawa.

Domin samun biyan buƙata kowace iri a wajen Allah duk yadda girman buƙatar ta kasance:

Ayi wannan Sirrin ta Bismillah da za mu kawo kamar haka: 

Za a karanta wannan addu'ar sau ɗari da goma sha takwas (118) sai ɗaga hannun a roƙi Allah buƙata:
 

بسم الله الرحمن الرحيم اللهم إني أسألك بفضل
بسم الله الرحمن الرحيم وبحق بسم الله الرحمن الرحيم وبهيبة بسم الله
الرحمن الرحيم وبمنزلة بسم الله الرحمن الرحيم ارفع قدري ويسر
أمري وأشرح صدري يا من هو (كهيعص) (حم عسق) (الم) (المص) (المر)
(حم) (الله لا إله هو الحي القيوم (بسر الهيبة والقدرة بسر الجبروت والعظمة
إجعلني من عبادك المتقين وأهل طاعتك المحبين وافعل لي كذا يارب
العالمين وصلى الله على سيدنا محمد وعلى آله الطيبين الطاهرين


Wannan addu'ar mujabbunce kada ayi kokonto A Jaraba a dogara ga Allah.

Allah ya sa mu dace.


 

إرسال تعليق (0)
أحدث أقدم