Gyambon ciki (Ulcer) ciwo ne da ake samu akan rufin ciki ko ƙananan hanji.
Mafi yawancin gyambon ciki (OLSA) yana faruwa ne a ƙananan hanji, irin wannan nau'in na olsa ana kiran ta a turance da duodenal ulcer. Olsa da take aukuwa akan rufin ciki ana kiran ta da gastric ulcers. Olsan dake ake samu a maƙogoro ana kiran irin wannan gyambon cikin (olsa) da esophageal ulcers.
ALAMOMI CIWON OLSA (GYAMBON CIKI)
* Rashin jin daɗi tsakanin abinci ko lokacin dare (uodenal ulcer).
* Rashin jin daɗi lokacin cin abinci ko sha (ulcer na ciki).
* Ciwon ciki wanda ke tasar mutum da dare.
* Kumburi, konewa ko jin zafi a ciki, hakan yana zuwa yana tafiya kwanaki ko makonni wani lokaci rashin jin daɗi yana ɗaukar mintuna ko sa'o'i ne sai ya wuce.
Idan gyambon cikinka (ulcer) yayi tsanani ya zama gyambon ciki mai fitar da jini. To zai haddasa alamomi kamar haka:
* Tashin Zuciya
* Amai da jini
* Raguwar nauyin jiki babu tsammani
* Kashi da jini ko kashi mai duhu
* Ciwon baya.
SAHIHIN MAGANIN ULCER (GYAMBON CIKI):
Da farko za a samu garin ƴaƴan gabaruwa da garin sassaƙen itacen Marke.
Garin ƴaƴan gabaruwa yafi yawa misali cokali goma shi kuma garin Marke cokali uku da rabi sai a haɗa guri guda a yamutsa sosai. Sai a rinƙa ɗiban ƙaramin cokali ana sha. Ko dai a sha da madara ko kunu ko a dafa a sha. Amma ba a son a sha cikin abin sha mai tsami.
Allah ya sa mu dace. Ku Jaraba kada kuyi kokonto.
Wassalamu Alaikum Warahamatullah Ta'ala Wabarakatuhu.🌹🌹🌹