DALILIN DAKE HADDASA RASHIN HAIHUWA.
Akwai dalilai da dama dake haddasa rashin haihuwa ga Maza da Mata. Ga wasu kaɗan daga cikin dalilan dake faruwa a ɓangaren Mace:-
- Toshewar kafar da mazakuta zata shiga.
- Budurci mai kauri wanda su ma'auratan ba su san yadda za su gusar da shi ba.
- Raɗaɗi da matan kan ji a lokacin saduwa. Dan haka bata bari maniyi ya shiga mahaifa anan ana bawa maigida Shawara da yayi amfani da man zaitun zai taimaka sosai.
- Sanya leda da ake yi a matsukin bututun da ƙwanta yake gangarowa yadda ba zai haɗu da maniyin mijinta ba.
Samun sinadarai masu kashe ƙwai ba shakka wannan matsukin kan samar da irin wanɗanan sinadaran.
- Bushewar mahaifa, samun kumburi a mahaifa, samun matsala a maƙyanƙyasar Mace ko kuma idan maƙyanƙyansar ta manne saboda yin wani aiki.
- Kitse mai yawa a gun dake tattara maniyi. Ko kuma haɗuwa da farin jini a matsukin mahaifa.
DALILAN RASHIN HAIHUWA ƁANGAREN NAMIJI.
- Matsalar maraina tun yaro yana ƙarami yana da kyau Uwa ta rinƙa binciken maraina ɗanta idan ta ji ba gudu ta yi saurin sanar da ƙwararren likata domin ɗaukan matakin da ya dace.
- Idan bututun da fitsari da maniyi suka samu matsala hakan na haddasa matsalar rashin haihuwa ga Namiji.
- Matsalar Ƙwai da kuma gwaiwa, shan wasu ƙwayoyi da Shaye-Shaye da kuma rashin saduwa a lokutan samun ciki.
- Rashin yin jima'i a lokutan ɗaukan ciki kasantuwar wasu maza suna ɗaukan lokacin kafin suyi jima'i wani na iya yin sati guda ko wata guda ko fiye da wata bai yi jima'i ba to idan hakan na faruwa sai aka yi rashin sa'a a duk lokacin da ya zo yin jima'i ya kasance ne a lokutan da ba na samun haihuwa ba. Hakan ka iya zama dalilin rashin haihuwa.
In Sha Allah a nan gaba zamu yi rubutu na musamman akan magungunan samun haihuwa. Ku ci gaba da Ziyartan Wannan shafin domin samun kyakkyawan shirye-shiryenmu masu matuƙar amfani.