ADDU'AR NEMAN KARIYA WAJEN ALLAH DAGA MAITA/MAYU.

 


ADDU'AR  NEMAN KARIYA WAJEN ALLAH DAGA MAITA/MAYU.


Al'amarin maita wani abu ne sananne a tarihi kuma wani abu ne da aka sani a Musulunci. Akwai ƙasashen duniya da dama da suke fuskantar wannan matsalar ta maita. Muma a nan ƙasashen Afrika ba a bar mu a baya ba mu kan fuskanci matsaloli da dama dake da alaƙa da maita,kambumbaka da Sihiri.Bincike yana nuni da cewa akwai ƙungiyar maita masu yawa a faɗin duniya kuma ita ma maita ƙungiyar asiri ce ko kuma muce suna da alaƙa na ƙud da ƙud.


Akwai nau'o'in maita a takaice kamar guda uku: 


1 Maita mai kisa: irin wannan maitar tana kisa ne. Sune waɗanda suke kama kurwar ɗan Adam su halaka.


2. Akwai masu ɓarna ko lalata mutum ko abin da ya mallaka. Irin wannan nau'in Maita idan suka sa ido a dukiyar mutum sai sun lalatata ma'ana sai dai a ga dukiyar na lalacewa.


3. Har ila yau akwai kuma Maita ta hassada wanda suke da tsananin hassada. Irin waɗannan Mayu ko mu ce masu irin wannan nau'in maitan ba su son su ga Allah ya yi wa wani ni'ima dan haka idan wani yana da wata ni'ima to za su yi amfani wannan maitar su gusar da ita.


Tambihi: Yana da muhimmanci mu fahimci cewa babu wanda zai iya cutar da wani ko kashe wani sai da izinin Allah.


ADDU'AR NEMAN KARIYA WAJEN ALLAH DAGA MAITA.

Idan kana tsoron cutarwar maye ko kuma kana wurin da akwai ire-iren waɗannan matsalolin to ka yi amfani da wannan addu'o'i da zamu kawo ƙasa:Ana so yawaita karanta wannan ayoyi na alƙur'ani mai girma domin neman kariya daga Maita. A ƙalla ka karanta safe da yamma kuma kana iya yin fiye da haka. Idan ka idar da karatun za ka ɗaga hannu ka roƙi Allah ya kare ka daga Sharrin Maita/Mayu. Kuma ana iya rubutawa a rataya duka dai domin neman kariya a wajen Allah.


Ga ayoyin kamar haka: 

بسم الله الرحمان الرحيم

إِنَّ فِي خَلْقِ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَاخْتِلَافِ اللَّيْلِ وَالنَّهَارِ وَالْفُلْكِ الَّتِي تَجْرِي فِي الْبَحْرِ بِمَا يَنْفَعُ النَّاسَ وَمَا أَنْزَلَ اللَّهُ مِنَ

 السَّمَاءِ مِنْ مَاءٍ فَأَحْيَا بِهِ الْأَرْضَ بَعْدَ مَوْتِهَا وَبَثَّ فِيهَا مِنْ كُلِّ دَابَّةٍ وَتَصْرِيفِ الرِّيَاحِ وَالسَّحَابِ الْمُسَخَّرِ بَيْنَ السَّمَا

 وَالْأَرْضِ لَآيَاتٍ لِقَوْمٍ يَعْقِلُونَ.

(سورة البقرة 164)


ۖ فَارْجِعِ الْبَصَرَ هَلْ تَرَىٰ مِنْ فُطُورٍ.

ثُمَّ ارْجِعِ الْبَصَرَ كَرَّتَيْنِ يَنْقَلِبْ إِلَيْكَ الْبَصَرُ خَاسِئًا وَهُوَ حَسِيرٌ.

وَإِنْ يَكَادُ الَّذِينَ كَفَرُوا لَيُزْلِقُونَكَ بِأَبْصَارِهِمْ لَمَّا سَمِعُوا الذِّكْرَ وَيَقُولُونَ إِنَّهُ لَمَجْنُونٌ. 

 وَمَا هُوَ إِلَّا ذِكْرٌ لِلْعَالَمِينَ 




قُلْ أَعُوذُ بِرَبِّ الْفَلَقِ  (1)  مِنْ شَرِّ مَا خَلَقَ  (2)  وَمِنْ شَرِّ غَاسِقٍ إِذَا وَقَبَ  (3)  وَمِنْ شَرِّ النَّفَّاثَاتِ فِي الْعُقَدِ  (4)  وَمِنْ

 شَرِّ حَاسِدٍ إِذَا حَسَدَ (5).


Allah ya sa mu dace.

Domin neman ƙarin bayani kuna iya tuntuɓarmu ta WhatsApp: +2347062014111

إرسال تعليق (0)
أحدث أقدم