DALILIN DA YA SA YAKE DA MUHIMMANCI MU RINKA SHAN HADIN CITTA MAI YATSU DA KURKUR AKAI-AKAI DA KUMA AMFANINSA GA LAFIYARMU

 

Saudayawa mu kan kasance tare da magani ba tare da mun sani ba, wani lokaci ma sai mu tafi nisa neman magani alhali ga magani a kusa da mu. Kodayake Malam Baushe ya yi gaskiya da ya ke cewa rashin sani yafi dare duhu. Da yardan Allah a wannan takaitaccen bahasin zamu kawo maku amfanin citta mai yatsu da kurkur ga lafiya dan Adam.

Yana da muhimmanci mu sani cewa samun waraka bai taƙaitu ga shan ƙwayan bature ko kuma magani na ruwa ba, da za mu rinƙa amfani da magungunanmu na asali,Misali yayan itatuwa, ganyaye da kuma wasu daga cikin nau'o'in abinci yadda ya kamata na iya yin dai-dai da manufar waƴancan magungunan na zamani kuma ya biya buƙatar da za su biya, tare da hana kamuwa daga wasu cututtuka da kuma samun waraka.

Wannan yasa yake da matuƙar muhimmanci mu duƙufa wajen nazari da bincike dangane da abubuwan gina jiki da kuma yadda za ayi amfani da su wurin samun waraka.


Ko shakka babu citta mai yatsu yana ɗaya daga cikin shahararrun itatuwa a fadin duniya. Ana amfani dashi sosai gurin dafa abinci kuma yana ƙara wa abinci ɗanɗano mai daɗi. Har ila yau ana amfani dashi wajen magunguna daban-danban kamar tashin zuciya, hana amai da sauransu. 

Kurkur {turmeric} a gafe guda itace ne da ake amfani dashi wurin maganin cututtuka daban-daban shima, saboda kasancewarsa yana da wadatar sinadarai dake yakar kumburi,daukan zafi da kayayyakin antioxidant sannan yana da  ɗanɗano yaji da kuma ɗaci. Hakan yasa ake amfani dashi a ko'ina a zaman kayan yaji don dafa abinci. Kodayake bincike ya nuna hada kurkur {turmeric} da citta mai yatsu a gauraya wanda shima yana da fa'ida ga lafiyar dan Adam.


1.  YANA RAGE KUMBURI/ZAFI/KUNA


Kumburi yana kara haɗari kamuwa da wasu cututuka kamar ciwon daji cututukan zuciya da kuma ciwon suga. Kurkur da citta mai yatsu suna da wadatattun sinadarai dake hana kumburi daukan zafi wanda ke taimakawa rage raɗaɗin ciwo da kuma kare jiki daga cututtuka. Wannan shi ne ya sa yana da kyau a rinƙa shan wannan hadin akai-akai. 


2.  YANA KARFAFA GARKUWAN JIKI



Wannan ƴaƴan itatuwan guda biyu wato citta mai yatsu da kurkur suna ƙunshe da abubuwan gina jiki da kuma ƙara lafiya, kuma idan ana cin su ko shan su daban-daban suna taimakawa wajen hana kamuwa da wasu cututtukan.Misali citta mai yatsu yana taimakawa wajen rage tashin zuciya, yayin da kurkur a gefe guda yana aiki don inganta lafiyar zuciya da yaƙar cutar Alzheimer wanda ke karuwa da shekaru. Idan aka sha kurkur da citta mai yatsu suna taimaka ma garkuwan jikin dan Adam.



3. YANA RAGE TASHIN ZUCIYA


Citta mai yatsu sannane da ɗanɗano kamar barkono, wanda yake taimakawa wajen daidaita ciki da kuma rage tashin zuciya. Shayin citta da kurkur kuma suna bada ɗanɗano barkono. 

BAYANIN MAGANIN INFECTION

إرسال تعليق (0)
أحدث أقدم