AMFANIN NA'A NA'A GA MASU FAMA DA CIWON ATHMA, CIWON MARA A LOKACIN AL'ADA

AMFANIN NA’A NA'A Na’a na’a na daya daga cikin tsirai da suke da matukar amfani ga lafiyar dan Adam, kamar dai yadda bicike ya tabbatar. A cikin wannan dan gajeren rubutun zai kawo maku wasu kadan daga cikin amfani na’a na’a ga lafaiyarmu. Sai dai babu laifi ana iya kara fadada binciken domin sanin wasu daga cikin amfanin wannan gayen mai albarka.Ga kadan daga cikin hanyoyin da ake amfani da na’a na’a sgayi: Bisa al’ada mata masu juna biyu kan yi fama da amai a yawan lokuta,idan aka samu ganyen na’a-na’a sai ta rinka taunawa duk safiya kafin ta karya Idan kuma yawan zubar da yawu ne, sai ta rinka barin shi a cikin bakinta na tsawon lokaci domin yana taimakawa wajen tsayar da yawu ( miyu ) ga mace mai juna biyu . Ga mai fama da gajiya ko kasala ,sai a samu na’a-na’a ana shakawa kadan-kadan , ko kuma a samu baho a zuba ruwan dumi a ciki a zuba man na’a-na’a a zauna a ciki kamar minti goma sha biyar (15) ko ashirin (20) . Mata da suke fama da ciwon mara a lokacin al’ada, a lokacin da ya fara sai a dafa ganyen na’a-na’a ta yi shayi da shi ta sha , zai rage tsanani ko kuma ya bari gada daya (ciwon) . Ga mai fama da mura, sai ta tami gayen na’a-na’ta rinka dafawa tana sha kamar shayi, ko da kuwa hanci ya toshe ne saboda mura sai a zuba na’a-na’a a ruwan sai ya shaki turiri da ke fita daga ruwan, za a samu sauki .Ana sa ran ko da cutar asma mutun yake da shi,yin haka na iya taimakawa wajen warkar da shi. Wasu masana na cewa ‘’Idan aka shuka itacen na’a-na’a a cikin gida in akwai mai cutar asma a cikin gidan zai warke. Ga mai fama da warin baki, ya rinka cin ganyen na’a-na’a sau uku (3) ko sau hudu (4) a mako zai taimaka sosai. Ga mai fama da kuraje fuska,a daka ganyen na,a –na,a kwaba da man shafawa a rinka shafawa ko a fuskar kadai ko kuman a jiki gaba daya. Ga mai fama da kumburin ciki, idan zai ci abinci ya tabbatar ya dafa ganyen na,a-na,a ya sha ruwan bayan ya ci abinci . Ga mai fama da shakuwa ya sami ruwan dumi kofi daya ya sa lemon tsami guda daya a ciki da gishiri dan kadan, da ganyen na,a-na,a ya sha, zai warke.

1 تعليقات

  1. Casinos Near Casinos Near Casinos - Mapyro
    Find the 출장샵 best casinos 경산 출장샵 near Casinos & 아산 출장안마 Hotels in Washington 상주 출장안마 State with MapYRO, the 당진 출장마사지 best place to get directions, reviews and information.

    ردحذف
إرسال تعليق
أحدث أقدم