No title

Wannan littafin/application Mai suna hanyoyin Waraka a Tafin Hannunka ta ƙunshi bayanai da suka shafi Sihiri da rabe-rabensa, maita,hassada da sauran cututtukan da al'umma ke fama da su da yadda za a magance waɗannan Cututtuka ta hanyar amfani da ayoyin Alkur'ani mai girma, addu'o'i da kuma magungunan gargajiya wanda aka daɗe ana amfani da su shekaru dubbai da suka gabata.

Na yi tunanin rubuta wannan littafin tare da haÉ—a wannan application É—in ne bayan na yi dogon na nazari cewa lallai al'ummar mu musamman al'ummar Musulmi masu amfani da harshen Hausa suna da buÆ™atuwa su san menene Sihiri?, maita, hassada da illolin da suke yi wa jama'a da kuma hanyar warware su. Bugu da Æ™ari a duniyar Musulunci an yi rubuce-rubuce da dama akan waÉ—annan cututtuka da harsuna daban-daban musamman ma harshen larabci amma mu anan  akwai Æ™aranci littatafan da aka rubuta su da harshen Hausa wannan ya sanya na É—auki abin rubutu da faÉ—a cikin bincike domin bada tawa guduwar abin da ya sauÆ™a.

Wannan littafin/application ta tattaro ayoyi Alkur'ani Mai girma da hadisai Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wa Alihi Wasallam) da kuma bayanai na malamai da yadda za a samu waraka daga cututtuka daban-daban da kuma addu'o'in nema biyan buÆ™ata da fita daga Æ™unci. A cikin wannan binciken mun yi amfani da gogayyar da muke da ita na  tsawon shekaru sama da ishirin (20yrs) muna bada maganin gargajiya (Islamic Medicine) hakan ya ba mu damar kawo hanyoyi da dama da muke amfani da su wa jama'a kuma suke samun waraka da iznin Allah Subhanahu Wata'ala. Dan haka wannan manhajar zata taimakawa jama'a sosai wajen magance Cututtukan da dama da kuma samun mafita daga matsalolinsu na yau da kullum.

Muna rokon Allah ya sanya aikin nan da muka yi ta zama karɓaɓɓe kuma ya kasance sadaƙatut-jariya garemu a bayan wafatin mu.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post