SIRRIN HASBUNALLAHU WA NI'IMAL WAKIL DOMIN SAMUN KARIYA DAGA SHARRUKAN MUTANE DA ALJANU.

 

 
SIRRIN HASBUNALLAHU WA NI'IMAL WAKIL DOMIN SAMUN KARIYA DAGA SHARRUKAN MUTANE DA ALJANU.


Wannan addu'a ce mai mutukar muhimmanci ana karanta ta ne  domin neman kariya a wajen Allah Subhanahu Wata'ala daga sharrukan Mahassada, masu sihiri da kuma dukkan sharrin Mutum dana aljani.

Duk wanda ya ke jin tsoron cutar mutane  ko kuma sharrukan Maƙiya da masu sihiri to ya lizimci karanta wannan addu'ar a ƙarshen kowace Sallah ko kuma ya rinƙa karantawa bayan sallar Asuba da kuma bayan sallar Isha'i.
 Da yardar Allah zai samu cikakkiyar kariyar Allah Subhanahu Wata'ala kuma sharrin Mutum ko aljan ba zai cutar da shi ba.

YADDA AKE YIN WANNAN ADDU'AR SHI NE:

A bayan kowace Sallah za karanta Hasbullahu Wa ni'imal Wakil. Ƙafa goma.

حسبنا الله ونعم الوكيل .  (عشر مرات).

  Bayan nan sai ka karanta wannan addu'ar ƙafa ɗaya ko uku ko kuma ƙafa bakwai. Ga Addu'ar kamar haka:

بسم  الله الرحمن الرحيم. حسبي الله لديني, وحسي الله لما أهمني وحسبي الله لمن بغي علي , حسبي الله لمن حسدني, حسبي الله لمن كادني بسوء, حسبي الله عند الموت, حسبي الله عندالشدة في القبر, حسبي الله عند المزان, حسبي الله عند الصراط حسبي الله لا الا هو عليه توكلت وليه أنيب.


Bismillah Rahmani Rahim. Hasbiyallahu Lidinii, Hasbiyallahu lima Ahammanii, wa Hasbiyallahu liman bugiya alayya, Hasbiyallahu Liman Hasadanii, Hasbiyallahu Liman Kadanii bisu'i, Hasbiyallahu indal-Maut, Hasbiyallahu indal-Shiddati fil-ƙabar, Hasbullah indal-Mizan, Hasbiyallahu indal-Siraɗi, Hasbiyallahu la'illahuwa alaihi tiwalaltu wa ilaihi uniib.
Post a Comment (0)
Previous Post Next Post