ISMULLAH A'AZAM DA AKE ROKONSA DA SHI A SAMU BIYAN BUKATA DA GAGGAWA

 

 

Idan kana son ka  roƙi Allah da Ismuhu-A'azam ka samu biyan buƙata da gaggawa.

Addu'a tana daga cikin hanyoyin nasara a rayuwa da kuma samun biyan buƙata. Kuma Manzon Allah tsira da Aminci Allah su ƙara tabbata a gare shi da iyalan gidansa ya koɗaitar da mu muhimmanci yin addu'a da kuma zurfafawa wajen yin addu'o'i, domin hakan zai ƙara kusantar da mu zuwa ga Allah,bugu da ƙari kuma za mu samu biyan buƙatocinmu. 
 Alƙur'ani Mai girma ya yi mana ishara da cewa Allah na da kyawawan sunaye mu roƙe shi da ita. Wannan yasa malamai sun yi bayanai daban-daban akan Ismullahi-A'azam wanda idan akan roƙe Shi da wannan suna za a samu biyan buƙata da gaggawa. 
 A cikin wannan taƙaitacce rubutun za mu kawo maku bayanin wasu daga cikin ayoyin Alkur'ani Mai Girma da Ismullah-A'azam ke cikinsu.
 An ruwaito daga Ali ibn Abu-Talib (Alaihi Salam) a cikin littafin da aka tattara addu'o'insa mai suna Sahifatul Alawiyya Jami'a yana cewa: '' Idan kana son ka roƙi Allah da Ismuhu-A'azam a ƙarɓa maka to ka karanta daga farkon suratul Hadidi zuwa wahuwa alimun ba zati-sudur, da kuma ƙarshe suratul Hashar daga lau'anzalna hazal Kur'ani ala jabali ...... Zuwa ƙarshen surah.
 Bayan ka kammala karatun zaka ɗaga hannu ka ce " Ya man huwa hakaza as'aluka bihaƙƙi hazihi as'ma'i an tusalli ala Muhammad Wa ali Muhammad. daga nan sai ka ambaci buƙatarka za a samu biyan buƙata da gaggawa. 

 Ga ayoyin Alkur'ani Mai Girma da ake karantawa mu fitar maku da su kamar haka:


بسم الله الرحمن الرحيم. سَبَّحَ لِلَّهِ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ ۖ وَهُوَ الْعَزِيزُ الْحَكِيمُ لَهُ مُلْكُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ ۖ يُحْيِي وَيُمِيتُ ۖ وَهُوَ عَلَىٰ كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ هُوَ الْأَوَّلُ وَالْآخِرُ وَالظَّاهِرُ وَالْبَاطِنُ ۖ وَهُوَ بِكُلِّ شَيْءٍ عَلِيمٌ هُوَ الَّذِي خَلَقَ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ فِي سِتَّةِ أَيَّامٍ ثُمَّ اسْتَوَىٰ عَلَى الْعَرْشِ ۚ يَعْلَمُ مَا يَلِجُ فِي الْأَرْضِ وَمَا يَخْرُجُ مِنْهَا وَمَا يَنْزِلُ مِنَ السَّمَاءِ وَمَا يَعْرُجُ فِيهَا ۖ وَهُوَ مَعَكُمْ أَيْنَ مَا كُنْتُمْ ۚ وَاللَّهُ بِمَا تَعْمَلُونَ بَصِيرٌ لَهُ مُلْكُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ ۚ وَإِلَى اللَّهِ تُرْجَعُ الْأُمُورُ . يُولِجُ اللَّيْلَ فِي النَّهَارِ وَيُولِجُ النَّهَارَ فِي اللَّيْلِ ۚ وَهُوَ عَلِيمٌ بِذَاتِ الصُّدُورِ . لَوْ أَنْزَلْنَا هَٰذَا الْقُرْآنَ عَلَىٰ جَبَلٍ لَرَأَيْتَهُ خَاشِعًا مُتَصَدِّعًا مِنْ خَشْيَةِ اللَّهِ ۚ وَتِلْكَ الْأَمْثَالُ نَضْرِبُهَا لِلنَّاسِ لَعَلَّهُمْ يَتَفَكَّرُونَ هُوَ اللَّهُ الَّذِي لَا إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ ۖ عَالِمُ الْغَيْبِ وَالشَّهَادَةِ ۖ هُوَ الرَّحْمَٰنُ الرَّحِيمُ هُوَ اللَّهُ الَّذِي لَا إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ الْمَلِكُ الْقُدُّوسُ السَّلَامُ الْمُؤْمِنُ الْمُهَيْمِنُ الْعَزِيزُ الْجَبَّارُ الْمُتَكَبِّرُ ۚ سُبْحَانَ اللَّهِ عَمَّا يُشْرِكُونَ هُوَ اللَّهُ الْخَالِقُ الْبَارِئُ الْمُصَوِّرُ ۖ لَهُ الْأَسْمَاءُ الْحُسْنَىٰ ۚ يُسَبِّحُ لَهُ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ ۖ وَهُوَ الْعَزِيزُ الْحَكِيمُ . 
ثم ارفع يديك و قل:* *يا مَنْ هُوَ هكَذا اَسْأَلُكَ بِحَقِّ هذِهِ الْاَسْماءِ اَنْ تُصَلِّيَ عَلى مُحَمَّدٍ وَ الِ مُحَمَّدٍ.* و سل حاجتك.

Domin neman karin bayani kun tuntubemu ta whatsapp: 2347062014111
Post a Comment (0)
Previous Post Next Post