ADDU’AR SAMUN MIJIN AURE/MATA DA KUMA SAMUN HAIHUWA

ADDU’AR SAMUN MIJIN AURE/MATA DA KUMA SAMUN HAIHUWA

Wannan addu’a ce ta musamman domin neman Allah ya azurta mutum da samun Mata ko kuma Mace da take neman Allah ya azurta da samun mijin aure nagari. Duk wadannan bangarorin guda biyu suna iya yin wannan addu’ar. Har ila yau wannan addu’ar ana yin ta domin neman samun haihuwa. Idan ma’aurata na neman haihuwa kuma Allah bai kaddara sun samu ba suna iya jarabta wannan addu’ar za su samu haihuwa da iznin Allah.


Dan uwa da Yar uwa masu daraja, idan za ku yi wannan addu’ar ku yi bisa yakinin samun biyan bukata kada ku sanya kokonto domin wannan addu’ar ta na cikin addu’o’i mujarrabai wato wanda aka gwada aka samu biyan bukata. Kai dai ka yi ka kuma dogara ga Allah ka jira biyan bukata tana hannunSa kada ka yi gaggawa.

GA YADDA AKE YIN WANNAN ADDU’AR KAMAR HAKA:

Da farko ana yin wannan addu’ar ne a juma’a ta karshe nawatan Ramadana bayan an yi alwallah an kali alkibla za a karanta suratul Daha kafa uku (wato surah ta ishirin a jerin surorin al-kur’ani mai tsarki). Sannan bayan kammala karatun suratul Daha kafa uku zaka karanta wannnan addu’ar dake kasa kafa daya. Bayan an kammala karanta addu’ar sai ambaci bukata shin aure ne ko kuma neman samun haihuwa. Za a dace da yarda Allah.

 

اِلـهي كَسْري لا يَجْبُرُهُ اِلاّ لُطْفُكَ وَحَنانُكَ، وَفَقْري لايُغْنيهِ اِلاّ عَطْفُكَ وَاِحْسانُكَ، وَرَوْعَتي لا يُسَكِّنُهااَمانُكَ، وَذِلَّتي لا يُعِزُّها اِلاّ سُلْطانُكَ، وَاُمْنِيَّتي لا يُبَلِّغُنيها اِلاّ فَضْلُكَ، وَخَلَّتي لا يَسُدُّها اِلاّ طَوْلُكَ، وَحاجَتي لا يَقْضيها غَيْرُكَ، وَكَرْبي لا يُفَرِّجُهُ سِوى رَحْمَتِكَ، وَضُرّي لا يَكْشِفُهُ غَيْرُ رَأفَتِكَ، وَغُلَّتي لا يُبَرِّدُها اِلاّ وَصْلُكَ، وَلَوْعَتي لا يُطْفيها اِلاّ لِقاؤُكَ، وَشَوْقي اِلَيْكَ لا يَبُلُّهُ إلاّ النَّظَرُ اِلى وَجْهِكَ، وَقَراري لا يَقِّرُّ دُونَ دُنُوّي مِنْكَ، وَلَهْفَتي لا يَرُدُّها اِلاّ رَوْحُكَ، وَسُقْمي لا يَشْفيهِ اِلاّ طِبُّكَ، وَغَمّي لا يُزيلُهُ اِلاّ قُرْبُكَ، وَجُرْحي لا يُبْرِئُهُ اِلاّ صَفْحُكَ، وَرَيْنُ قَلْبي لا يَجْلُوهُ اِلاّ عَفْوُكَ، وَوَسْواسُ صَدْري لا يُزيحُهُ اِلاّ اَمْرُكَ، فَيا مُنْتَهى اَمَلِ الاْمِلينَ، وَيا غايَةَ سُؤْلِ السّائِلينَ، وَيا اَقْصى طَلِبَةِ الطّالِبينَ، وَيا اَعْلى رَغْبَةِ الرّاغِبينَ، وَيا وَلِيَّ الصّالِحينَ، وَيا اَمانَ الْخائِفينَ، وَيا مُجيبَ دَعْوَةِ الْمُضْطَرّينَ، وَيا ذُخْرَ الْمُعْدِمينَ، وَيا كَنْزَ الْبائِسينَ، وَيا غِياثَ الْمُسْتَغيثينَ، وَيا قاضِيَ حَوائِجِ الْفُقَراءِ وَالْمَساكينَ، وَيا اَكرَمَ الاَْكْرَمينَ، وَيا اَرْحَمَ الرّاحِمينَ، لَكَ تَخَضُّعي وَسُؤالي، وَاِلَيْكَ تَضَرُّعي وَابْتِهالي، اَسْاَلُكَ اَنْ تُنيلَني مِنْ رَوْحِ رِضْوانِكَ، وَتُديمَ عَلَيَّ نِعَمَ امْتِنانِكَ، وَها اَنـَا بِبابِ كَرَمِكَ واقِفٌ، وَلِنَفَحاتِ بِرِّكَ مُتَعَرِّضٌ، وَبِحَبْلِكَ الشَّديدِ مُعْتَصِمٌ، وَبِعُرْوَتِكَ الْوُثْقى مُتَمَسِّكٌ، اِلـهي اِرْحَمْ عَبْدَكَ الذَّليلَ ذَا الّلِسانِ الْكَليلِ وَالْعَمَلِ الْقَليلِ، وَامْنُنْ عَلَيْهِ بِطَوْلِكَ الْجَزيلِ، وَاكْنُفْهُ تَحْتَ ظِلِّكَ الظَّليلِ، يا كَريمُ يا جَميلُ يا اَرْحَمَ الرّاحِمينَ.

اللَهُمً إِنِّي أَسُألُكَ بِقُدْرَتِكَ الَّتِي تَغَيَيرَ بِهَا الأَشْيَاءَ, اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ بِعِزَّتِكَ وَجَلآلِكَ وَهَيْبَتِكَ وَعَظِيمُ قُدْرَتِكَ وَفِي مَعْقَلِ عِزَّكَ وَأَسْأَلُكَ بِاسْمُكَ الًذِي تَقُولَ بِهِ لِلْشَيْءِ كُنْ فَيَكُونَ أَسْأَلُكَ أَنْ تُصًلِّي عَلًى مُحَمَّدٍ وَآلِ مُحَمَّدٍ وًأَنْ تَجْعَلْ لِي فَرْجًا بِالصَّلَاةِ عَلَى مُحَمَّدٍ وَآلِ مُحَمَّدِ.....(

رَبِّ لَا تَذَرْنِي فَرْدًا وَأَنْتَ خَيْرُ الْوَارِثِينَ)


 TAMBIHI: A duk lokacin da muke addu’a mu halarto da zuciyarmu wajen addu’ar tare da Kankan da kai da khushu’i ga Allah Madaukakin Sarki kuma mu guji yin gaggawa wajen ganin biyan bukata domin Allah Shi ka dai ke biyan bukata kuma ya fi mu sanin maslaha idan ya jinkirta ba a mu abinda muka roka da wuri ba .

Tuntuba: kuna iya tuntubarmu ta whatsapp a wannan nambar: +2347062014111


 

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post