SIRRIN KULLA SOYAYYA MAI ƘARFI MUJARRABUN




SIRRIN KULLA SOYAYYA MAI ƘARFI.


Da farko yana muhimmanci mu fahimci cewa ita soyayya daga Allah take abin nufi anan shi yake sanya soyayyar wanda ya so a cikin zuciyar wanda ya ga dama.


 Idan Allah ya so sai ya sanya soyayyarka a cikin zuciyar wani idan kuma yaso sai ya kasance ko da kai  kana son mutum sai ka ga shi baya sonka kwata-kwata.


 Kuma ko da zaka bayar da abin da yake cikin duniya gaba ɗaya ba zai so ka ba. Idan kuma ya so sai ya sanya maka soyayyan jama'a ko kuma wani mutum koda kuwa baka da komai. Misali:  A cikin suratul Daha aya ta talatin da tara (39) Allah yayi nuni da cewa shi ne ya sanya soyayyar Annabi Musa (a.s) a cikin zuciyar Fir'auna duk kuwa da cewa a daidai wancan lokacin idan aka haifi Ɗa namiji Fir'auna (L) ya kan ba da umurni a yanka shi. Amma da aka haifi Annabi Musa (a.s) sai Allah ya sanyawa Fir'auna da iyalansa ƙaunar Annabi Musa (a.s).


Ga abinda ayar take cewa : 


...... ۚ وَأَلْقَيْتُ عَلَيْكَ مَحَبَّةً 

مِنِّي وَلِتُصْنَعَ عَلَىٰ عَيْنِي 


Allah ya ce: .....Kuma na sanya maka soyayya daga wajeNa kuma don arene ka akan idona.


Da wannan misalin da kuma wasu ayoyi da dama a cikin alƙur'ani da suke nuni da cewa ita soyayya daga wajen Allah take shi kuma shi Ne asalinta na haƙiƙa. Idan mun fahimci haka to ya zama wajibi idan muna neman soyayya ko a ƙaunace mu to mu koma mu neme ta a Wajen Allah Subhanahu Wata'ala.


Don haka ya zama wajibi mu nisanci zuwa wajen matsafa ko bokaye idan muna neman soyayya ko mallakan wani,saboda ko ba komai ai ita soyayya a gurin Allah take kuma muna iya nemanta a wajenSa ta hanyar roƙonsa da addu'o'i.


 Idan mu na son a so mu to koma wajen Allah muna  masu ƙanƙan da kai da kuma magiya har lokacin da Allah zai amsa mana kokenmu ya biya mana buƙatarmu ya sanya soyayyarmu a cikin zuciyar wanda muke so ya so mu.


ADDU'AR SAMUN SOYAYYA:


A takaice zan kawo maku bayanin yadda zaka samu soyayya daga Allah akan duk wanda kake so ya so ka.


Da farko: Duk bayan sallar asuba ka karanta wannan ayar dake cikin suratul Yasin ayat ta 72 ƙafa ɗari. Ga ta kamar haka:

 وَذَلَّلْنَاهَا لَهُمْ فَمِنْهَا رَكُوبُهُمْ وَمِنْهَا يَأْكُلُونَ.

TANBIHI; Za ayi ta maimaita wannan addu'ar har buƙata ta biya. 


Na biyu: Harwayau ana tofa ita wannan ayar ta suratul Yasin aya ta72 (wato wanda muka ambata a sama) ƙafa 70 a cikin duk wani abu mai zaƙi (kamar dabino, lemu, rake dss) aba wanda ake so ya ci. Ku jaraba kada ku yi kokonto. Allah ya amshi addu'o'inmu.

Domin karin bayani kuna iya tuntubarmu ta whatsapp: +2347062014111

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post