SIHIRIN SOYAYYA, YADDA AKE KULLAWA DA KUMMA YADDA AKE WARWARE SHI


SIHIRIN SOYAYYA.

Daga cikin nau’o’in sihirin da ake ƙullawa akwai sihirin soyayya. Yawan samun saɓani tsakanin mata da miji ko saurayi da budurwa na daya daga cikin dalilan dake haddasa aikata irin wannan sihirin.

Akwai wasu sashen mata da idan suna yawan samun saɓani/faɗa ko kuma suka lura da cewa akwai ƙarancin soyayya tsakaninsu da mazajensu,ba za sa iya haƙuri dan haka suke garzayawa zuwa wajen boka ko mai sihiri domin ya kulla masu sihiriin da mijinsu zai so su sosai,sai yadda su ka yi da shi. Wannan na faruwa ne saboda karancin riƙo da addini a janibin ita matar ko kuma jahiltarta da sanin cewa wannan abinda ta aikata haramun ne.

YADDA AKE ƘULLA SIHIRIN SOYAYYA.

Shi wannan mai sihirin ko bokan zai buƙaci ita matar ta kawo masa wani abu na suturan mijinta. Misali: hankacif ɗinsa wanda bai wanke ba, rigarsa, wandonsa, kasar tafin kafansa da sauransu daga nan sai bokan ya haɗa mata wannan sihirin na soyayya ko mallakan miji. Wasu idan sun haɗa sihirin sukan umurci matar da ta sanyawa mijin a abinci ko abin sha. Wasu bokayen kuma su kan umurci matar da ta kawo jinin al’adarta su haɗa sihirin da shi bayan sun hada sai ta sanya wa mijin a abinci ya ci. Wa su kuma su kan buƙaci su yi rubutu a farjin matar da take son a hada mata irin wannan nau'in sihirin ko kuma suce sai sun sadu (zina) da ita. Wa iyazu billlah. Wannan a bayyane ta ke ga kowa cewa sabon Allah ne karara.

ALAMOMIN DA KE NUNI DA ANYI WA MUTUM SIHIRIN SOYAYYA.

- Matsanancin soyayya da ya zarce na al’ada

- Matsananci son yin jima’i.

- Rashin haƙuri idan ba ka ga matar ba.

- Tsananin son ganinta. 

-Makauniyya biyayya gare ta.

DALILAN DA KE HADDASA SIHIRIN SOYAYYA 

1-Yawan samun saɓani tsakanin ma’aurata. Idan mace tana yawan samun matsala da mijinta idan akwai ƙarancin tsoron Allah kuma ta haɗu da kawayen banza da kuma rashin sanin addini wannan  na daga cikin dalilan dake sanya mace ta je wajen boka ayi mata sihirin soyayya.

2- Kodayin dukiyan Miji musamman idan mijin na da dukiya yana daga cin dalilan da ke sanya mace ta je wajen boka don ta mallaki mijin da dukiyarsa.

3. Kishi mai Matsanani: Idan Mace na da tsananin kishi kuma tana tsoron mijinta ya yi mata kishiya wannan kan sanya mace ta je wajen boka ayi mata sihirin soyayya.

SIHIRIN DA YA HALITTA 

Yana da muhimmanci Mata muminai su sani akwai hanyoyin mallakar miji da samun soyayyar miji da ya halitta wanda ba sai an je wajen boka ko mai sihiri ba.

Kadan daga ciki shi ne mace ta kasance mai yawan ado da kuma tsafta ta yawaita bayayyar kyauwunta ga mijinta. Har iyala yau yana da kyau ta zamo mai ladabi da biyayya da kuma iya magana ga mijinta da kuma kula da dukiyarsa da yayansa kuma ta rinka kyautawa iyayen miji da ya uwansa. Ta yawaita sanya turare da kayan ƙamsasa daki. Sannan babu laifi ta hada da addu’o’i da suka halitta na bangaren soyayya.

 YADDA AKE WARWARE SIHIRIN SOYAYYA.
Ana karanta ayoyin Alqur'ani a cikin ruwa ana sha. Ga ayoyin kamar haka:

Suratul Fatiha  ƙafa 70
Suratul Falaq ƙafa 70
Suratul Nasi 79


 

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post