Yadda ake
kulla Sihirin hana Mace Aure da kuma yadda ake warware shi.
Maketaci kuma makirin Mutum mai hassada ya kan je wajen mugun boka ko mai sihiri, ya nema ayi
masa aikin da zai hana yar wani (wato wanda yake so ya hana ta yin aure), shi
kuma wannan mugun bokan zai nemi ya fada masa sunan yarinyar da na mahaifiyarta
da kuma wani yanki na suturanta ko kasan tafin kafanta ko wani abu mai kama da
haka.
Sai wannan
mugun bokan ya fara yi masa aiki na sihiri wanda zai wakilta aljani ko aljanu
domin gudanar da wannan aikin. Sai wannan aljani ya shiga jikin wannan matar
kuma zai kasance tare da ita a kodayaushe sai ya sanya mata wadannan matsaloli
guda hudu da zamu ambata kamar haka:
1- Tsoro mai
tsanani
2- Fushi mai
tsanani (saurin yin fushi)
3- Mantuwa
mai tsanani
4- Aukawa
cikin sha’awa
-
Kodai ya sanya wa mace wanda akayi wa wannan nau’in
sihirin ta rika jin kunci da damuwa ga duk namijin da ya zo nemanta da aure wanda
hakan zai sa ta ji bata sonshi kwata-kwata har ta kore shi ya daina zuwa
wajenta.
-
Idan kuma hakan bai yiwu masa ba, wato bai iya shiga
jinkinta ya yi mata wannan illar ba to sai ya fito mata daga waje wato sai ya
rika sanya maza su rinka ganinta da mummunan kama suna kyamanta ba sa ganin
kyauwunta kwata-kwata,wannan zai sabbaba ta rasa mijin aure.
Har ila yau
ya kan sa mace ta rinka koran duk wani namiji da ya zo wajenta da maganar aure ba
tare da wani dalili ba. Idan yanayin sihirin yayi tsanani da zaran namiji ya je
gidan matar da suna aure zai ji kunci sosai zai shiga damuwa fuskanshi zata
canza zai ji kamar yana cikin kurkuku sanadiyan haka ba zai sake komawa gidan
ba.
ALAMOMIN SIHIRIN HANA MACE AURE:
1- Yawan
ciwon kai nan da can wanda ko da an sha magani ba a warkewa.
2- Kuncin
mai tsananin a cikin kirji musamman bayan la’asar zuwa tsakiyan dare.
3- Zata
rinka ganin duk wanda yake nemanta da muni (mummunan kama) ta yadda zata ji
bata kaunarshi.
4- Yawan
tunani
5-Yawan jin
tsora da shiga damuwa a cikin bacci (kwana)
6- Wani
lokacin zata rika jin radadi a uwan hanji a kodayaushe.
7- Za ta
rika jin ciwon baya daga kasan bayanta.
YADDA ZA MAGANCE WANNAN MATSALAR:
Akwai
hanyoyi da dama na warware wannan sihirin kuma zamu fadi kadan daga cikin kamar
haka:
1- Ana
warware wannan sihiri ta hanyar rukiyya ma’ana a karanta mata wasu daga cikin
ayoyin alkur’ani idan alamun aljani ya bayyana a tare da ita ayi magana da shi
a raba shi da jikinta kuma a bata maganin da zata yi ta amfani da shi.
2. Mace mai
mafa da irin wannan lalura ana so a kodaushe ta lizamci sanya hijabi na shari’a.
3- Ta kiyaye
salla akan lokaci
4- Ta rika
alwala kafin ta kwanta bacci da karatun ayatul kur’siyyu.
5- Ta daina
sauraren kide-kide/music da raye-yare.
-
Ta hada tafin hannuwanka guda biyu ka karanta falaq da
Nasi ka tofa shafa jikinka sauku.
-
Kullum ta saurari sautin karatun ayatul kursiyyu
-
Ta karanta ayoyin rukiyya a cikin ruwa tana sha ta yin
wanka sau uku a rana.
-
Ta kiyaye yin azkar a kullum