MAGANIN SAMUN HAIHUWA.


Kamar yadda muka yi bayani a rubutun da ya gabata cewa akwai dalilai daban-daban dake haddasa rashin haihuwa wasu daga ciki suna da alaƙa da matsalolin aljanu wasu kuma matsaloli ne na daban wanda mun yi bayanin wasu daga cikinsu.


Akwai magunguna da dama na gargajiya da na Musulunci wanda idan aka yi amfani da su za a samu haihuwa. Idan Allah ya yarda. 


Amma saboda kada rubutun ya yi tsayi za mu kawo maku ɗaya daga cikin maganin samun haihuwa.


INGANTACCEN MAGANI SAMUN HAIHUWA:


Da farko za a samu garin tafarnuwa cokali biyar , hulba cokali biyar, albabunaj cokali uku da fijil cokali biyu sai a haɗa su cikin zuma kwalba uku sai a ɗora a kan wuta mara ƙarfi har sai ya haɗe , sai a rinƙa shan cokali biyu sau uku a yini har ya ƙare. Da iznin Allah za a samu haihuwa. Allah ya sa mu dace.


Domin neman ƙarin bayani ku tuntuɓemu ta WhatsApp : +2347062014111

 

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post