MAGANIN KARATU TARE DA SAMUN HADDAR ALƘUR'ANI FISABILILLAH.




MAGANIN KARATU TARE DA SAMUN HADDAR ALƘUR'ANI FISABILILLAH.

Sau da yawa wasu kan yi mafa da matsalar saurin mantuwa ta yadda wani lokaci idan sun ajiye abu sai su manta da inda suka ajiye ko kuma idan aka yi alƙawari da su sai su manta wanda idan hakan na faruwa to tabbas za su iya mantawa da wasu abubuwa masu matukar muhimmanci. Kuma hakan na ayi kaiwa zuwa ga hasara abubuwa da dama, ko ya kai a aukawa cikin matsaloli.

Wasu kuma Ɗalibai ne masu neman ilmi da suke karatu tun daga matakin farko, Wato yanzu suka fara karatun amma kasantuwa ko sunyi karatun basa ganewa hanka ke sanyawa su yi watsi da karatun kwata-kwata, tun ba a kai ko ina ba su zaɓi zama a cikin jahilci. Duk kuwa da cewa yin hakan bai da ce domin da sunyi hakuri sun ci gaba da addu'a da neman ilmin da wata rana Allah ya bude masu kwakwalwarsu sun samu ilmi mai yawa.

Wasu kuma sun yi karatun sun kai ga matakin samun gurbin karatun a jami'a amma sanidiyar rashin gane karatu yakan kai ga an kore su da jami'ar wato saboda ba su kai ga matakin da ake buƙata ba.

Harwayau, wasu kuma suna karatu ne a bangaren neman ilimi Addinin Musulunci Misali haddar alƙur'ani. Amma saurin mantuwa da rashin riƙe Karatu na basu wahala sosai. 

In Sha Allah idan aka lizimci wannan Addu'ar da za mu yi bayanin zaka daina mantuwa kwata-kwata kuma zaka rinƙa saurin gane karatu tare da samun ƙarfi hadda.

Wannan itace addu'ar da Manzon Allah Sallallahu alaihi Wa Alihi Wasallama ya sanar da Imam Ali (a.s).

Addu'a ce ta samun kaifin basira da rashin mantuwa. Ga Addu'ar kamar haka:

سُبْحانَ مَنْ لا يَعْتَدِي عَلى أَهْلِ مَمْلَكَتِهِ, سُبْحانَ مَنْ لايَأْخُذُ أَهْلَ الاَرْضِ بِأَلْوانِ العَذابِ, سُبْحانَ الرَّؤُوفِ الرَّحِيمِ ».اللَّهُمَّ اجْعَلْ لِي فِي قَلْبِي نُوراً وَبَصَراً وَفَهْما وَعِلْماً إِنَّكَ عَلى كُلِّ شَيٍ قَدِيرٌ

 

Subhana Manlaya'atadi ala ahli Mamlakatihi, Subhana  Manlaya'akhuzu ahlal-ardi  bi alwanil-azabi, Subhana Ra'ufir-Rahim.

 {{ Allahumma Ij'al fi ƙalbi nuran wa basaran wa fahman wa ilman innaka ala kulli shai'in ƙadir}}.

Wannan addu'ar za a rinƙa karanta ƙafa uku bayan idar da sallolin farilla. Za a samu ilimi tare da saurin hadda na ban mamaki. In Sha Allah.  

 

 Tambihi: idan kun ga kuskure daga garemu yake.Kuma kuna iya ba da shawara. Mun gode.

Domin neman ƙarin bayani kuna iya tuntuɓarmu ta nambarmu a WhatsApp +2347062014111


 

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post