Cutar hanta (Hepatitis) ƙwayan cuta ce da dake haddasa kumburin hanta. Kuma ana kamuwa da ita wannan cutar ce ko dai ta hanyar jima'i (wato saduwa), ko allura da akayi amfani da shi ga wani mai ɗauke da ita wannan cutar. Kuma ana kamuwa da ita ta hanyar ƙarin jini wato idan aka ƙara wa mutum jini kuma wannan jinin na ɗauke da wannan cutar.
Har ila yau ana kamuwa da ita ta hanyar shan giya ko ko miyagun ƙwayoyi ba bisa ƙa'ida ba.
IRE-IREN CUTAR (HEPATITIS):
Akwai nau'o'in cututtukan hanta kamar haka:
Hepatitis A,hepatitis B, hepatitis C, hepatitis D, hepatitis E.
ALAMOMIN CUTAR HANTA (HEPATITIS)
Idan mutum na ɗauke da ɗaya daga cikin nau'ukan cutar hanta kamar hepatitis B da hepatitis C ba safai yake nuna alamar ba har sai yayi illa babban ga hanta. A taƙaice mutane da suke ɗauke da cutar hanta ka iya jin waɗannan alamomi kamar haka:
* Jin gajiya ko da kuwa ba ayi wani aiki ba
* Fitsari mai duhu
* Ciwon jiki
* Rashin son cin abinci
* Rama sosai
* Fata da ido su koma ruwan Kore.
MAGANIN CUTAR HANTA
Akwai hanyoyi da dama da za a iya bi wajen magance cutar hanta. Kuma akwai magunguna da dama da za a iya amfani dasu domin maganin cutar hanta. Kodayake yana da matuƙar muhimmanci a tuntuɓi ƙwararru a ɓangaren lafiya domin tantancewa da kuma ba da shawara akan Maganin da yafi dacewa ayi amfani da shi kasancewar ita wannan cutar tana da nau'o'i daban-daban kamar yadda muka ambata a baya.
Wannan maganin da za mu ambata yanzu yana ɗaya cikin magungunan ciwon hanta mai matuƙar tasiri wanda sau da dama anyi amfani da shi an warke.
Da farko za a nemi garin hulba cokali goma, garin ɓaure cokali goma sai ya cakuɗasu guri guda a riƙa ɗinba cokali a na dafawa cikin ruwa ƙaramin kofi ana sanya zuma cokali biyu ana sha sau uku a rana.
Kuna iya tuntuɓarmu ta WhatsApp +2347062014111
Muna fatan za ku ji daɗin amfani da wannan magani. Wassalamu Alaikum Warahamatullah Ta'ala Wabarakatuhu.