SALLAR
KUN-FAYAKUM, WANNAN SIRRIN MUJARRABUN CE A WAJEN MALAMAI.
Ana kiran
wannan Sallar da Sallar kunfayakun kuma ana yinta ne akan kowace bukata da
Shari’ah ya yarda da ita.
Yadda ake
yin wannan Sallar: Zaka yi alwala ka yi sallan Nafila raka’a hudu a jare da
sallama guda.
1- Raka’an
farko za a karanta fatiha da wannan ayar da zamu kawo kafa dari (100)
ۚ وَأُفَوِّضُ أَمْرِي إِلَى اللَّهِ ۚ
2- A raka’a ta biyu bayan karatun Fatiha zaka karanta wannan ayar kafa
dari (100):
نَصْرٌ مِنَ اللَّهِ وَفَتْحٌ قَرِيبٌ ۗ
A raka’a ta biyu zaka zauna ka yi tahiya amma ba za kayi sallama ba,
idan ka gama zaka mike kawo raka’a ta uku. A raka’a ta uku zaka kawo karatun
fatiha da wannan ayar kafa dari (100):
ۗ أَلَا إِلَى اللَّهِ تَصِيرُ الْأُمُورُ
A raka’a ta hudu za a karata suratul fatiha da wannan ayar kafa dari
(100):
إِنَّا فَتَحْنَا لَكَ فَتْحًا مُبِينًا
Bayan ka kammala salla da sallama za karanta wannan istigfarin sau dari
(100).
أستغفر الله ربي وأتوب إليه.
TAMBIHI: Bayan an kamala
za a daga hannu a roki Allah bukata. Ku yi kada ayi kokonto. Allah ya mu dace.
Tuntubarmu: Whatsapp: +2347062014111.