ILLAR DA CUTAR TYPOID KE YI WA DAN-ADAM DA KUMA HANYOYIN DA ZAMU KARE KANMU DAGA KAMUWA DA ITA.

 


ZAZZABIN TYPOID:

Wannan wata cuta ce da ta yaɗu a duniya har ta zama kusan gidan kowa akwai sakamakon ƙwayar cutar ana kamuwa da ita ne ta hanyar cin gurbataccen abinci ko kuma gurbataccen ruwa.

Taifot ƙwayar cuta ce da ka iya yin mummunar ɓarna a ɓangarori da daman na jiki, idan a ba a ɗauki matakin yin magani da gaggawa ba. Harwayau, yana da muhimmacin yin maganin wannnan cutar da wuri domin tana haddasa illar da ka iya kai ga rasa rayuwa.

Zazzaɓin taifot cuta ce mai rikitarwa da kuma kin jin magani wato ina nufin mutum na iya tashan magani ba tare da ya samu waraka da sauri ba. Hakan yasa yake da muhimmanci mu yi iya ƙoƙarinmu wajen kaucewa hanyoyin kamuwa da wannan cutar.

Kamar yadda muka ambata a baya ita wannan cutar tana faruwa ne,sanadiyar wata ƙwayar cuta da ake kira "Salmonella Typhi"  wanda yake yaɗuwa ta hanyar abinci ko ruwan dake ɗauke da wannan cutar ko cuɗanya ta kai tsaye da mutumin dake ɗauke da wannnan cutar.

Duk kuwa da cewa zazzaɓin taifot ta yadu kusan sassa da dama a faɗin duniya to amma ana iya cewa tafi yaɗuwa a ƙasashen Afirka, Indiya, Asiya ta kudu da Amurka ta kudu.


KU DANNA WANNAN LINK DIN DOMIN SAUKE MANHAJARMU MAI SUNA KOWACE CUTA DA MAGANINTA


ALAMOMIN DA KE NUNI DA CEWA MUTUM NA ƊAUKE DA ZAZZAƁIN TAIFOT.


 i. Cutar zazzaɓin taifot ta kan haddasa: [a] zafin jiki [b] ciwon kai da ciwon ciki wani lokaci [c] sanyi da kuma busasshen tari.


ii. Idan ba a dauki matakin gaggawa ba bayan wani lokaci, jiki kan ƙara tsananin zafi sosai ta yadda jijiyoyi ma za a ji suna raɗaɗi har yasa ƙwannafi kaɗan-kaɗan, da ciwon haƙarƙari, daga nan kuma sai zawo, wannan duk ya fi tsanani da yamma zuwa cikin dare.


iii. Har ila yau zazzabi zai ci gaba da yin tsanani dukkan alamomin nan da aka fada zai kara tsanani babu kakkautawa tare da tsananin kasala.


Ga kadan daga cikin wasu hanyoyin da za su taimaka wajen dakile yaduwar cutar a kasashe masu tasowa.

1. Shan ruwan kwalba [bottle water]

2. Kula da tsafta da kuma tsaftace muhalli.

3. Mu guji cin abinci ko abin shan da wani ya sarrafa kasancewar ba mu da masaniya ko wanda yayi abinci ya ɗauke da wannan cutar.

4. idan babu ruwan kwalba to a tabbatar an tafasa ruwan sha da kyau kafin a sha.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post