AMFANI JINI A JIKI DA KUMA ALAMOMIN ƘARANCINSA A CIKIN JIKI.



 Jini na da matukar muhimmanci a cikin jikin ɗan Adam. Mutane ba za su iya rayuwa ba tare da jini ba, idan babu jini a jiki gaɓoɓi ba za su iya samun iskar oxygen da abubuwan gina jiki da suke buƙatar rayuwa ba. Domin idan babu jini ba za mu iya ɗaukar ɗumi ko sanyi ba, ko yaƙar cututtuka dake kama jikin ɗan Adam, ko kuma fitar da abubuwa mara amfani a jiki ba.


Tabbas ƙarancin jini na iya sanya mutum ya raunana ko ma tai ga iya rasa ransa gaba ɗaya. Dan haka ne yake da muhimmanci musan alamomin ƙarancin jini a jikin ɗan Adam domin daukan matakin gaggawa ta hanyar zuwa asibiti idan muka ji ɗaya daga cikin waƴannana alamomin.

Domin samun cikakken bayani game da alamomin ƙarancin jiki ku shiga wannan link da za mu a jiye maku a ƙasa: 

https://youtu.be/NBLbT5mzu0w


YADDA JINI KE ZAGAYAWA A JIKI ƊAN ADAM:

A kowace bugun zuciya, zuciya tana bugun jini ya isa ko'ina a cikin jikinmu, yana ɗauke da iskar oxygen, jinin ya koma zuciya.

Zuciya sai ta aika da jini zuwa huhu dan ɗaukar ƙarin iskar oxygen. Wannan sake zagayowar yana maimaitawa akai-akai.


 

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post