ABUBUWAN DA KE SANYA A ƘARƁI ADDU'A DA GAGGAWA.

 


DALILAN KARƁAR ADDU’AR DA GAGGAWA.


Addu’a ganawa ce tsakanin Bawa da Mahaliccinsa kuma tana ɗaya daga cikin Ibadoji masu muhimmanci a addinin Musulunci. Allah Maɗaukakin Sarkin ya Umurci BayinSa da su roƙe Shi kuma yayi alƙawarin karɓa masu kamar yadda ya zo a cikin Al-kur’ani mai girma a cikin suratul Gafir aya ta 60 ‘’ Kuma Ubangijinku ya ce ku roƙeNi in karɓa maku.. ‘’ Kuma harwayau a wani ayar yana cewa ‘’ Ina amsa kiran mai kira idan ya kira Ni…’’ . Manzo Allah tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare da iyalangidansa ya ƙarfafamu akan yin addu’a a cikin zantukansa masu albarka har ma an ruwaito yana cewa: "Allah na fushi da wanda baya riƙonSa".


WASU ABUBUWAN DAKE HANA KARBAR ADDU’A.


Lomar Haram: abin nufin anan shi ne cin haram ko shan haram ko sanya suturar da aka saya da kuɗin haram suna hana a karɓi addu’armu. Har ilaya yau munanan ɗabi’u na hana karɓar addu’a kamar girman kai, hassada, rowa, zalunci da giba (yi da mutum) duk waɗannan ɗabi’un da muka ambata suna hana karɓar addu’a.


Miyagun ayyuka suna hana karɓar adddu’a, kamar cin haƙƙin mutane da bushewar zuciya,da rashin kamun kai da ƙwatar guri ko sutura duk suna sanya a ƙi karɓar addu’a ko kuma shakka akan samun biyan buƙata da kuma yanke ƙauna. 


DALILAN DA KE SA A SAMU BIYAN BUƘATA DA GAGGAWA.


1. Tsarki: Ana so idan zaka yi addu’a ka yi alwala ko wanka kuma kasan sutara mai tsarki babu laifi idan mutum zai yi addu’a ya ci ado saboda addu’a ganawa ne tsakanin Bawa da Mahalaccinsa da haka ya kamata ya kasance cikin kyakkawan sutura.


2. Hallarto da zuciya a lokacin addu'a. Ana son mai addu’a zuciyarsa ya kasance a gurin Allah, ya maida hankalinsa akan addu’ar da yake yi kuma ya fuskantar da tunaninsa ga Allah Madaukakin Sarki. Kada ya kasance yana addu’a zuciyarsa na wani gurin. Idan zai yiwu ya rinƙa tunanin akan abin da addu’ar ya ƙunsa ma’ana akan abinda yake karantawa a cikin addu'a.


3.Wurin yin addu’ar. Akwai wurare masu falala waɗanda idan aka yi addu’a a waɗannan wurare ana samun ijaba da gaggawa, kamar masallatai da Harami da sauransu. 


4. Lokuta Masu falala. Akwai wusu lokuta kiɓantattu da suke da falala na musamman kuma lokuta ne na karɓar addu’a. Misali kamar ranar Arfa, lokutan sahur da lokocin faɗuwar rana da lokocin fitowar rana {Bayan Sallar Asuba}. Da kuma watan Ramadan da lokacin buɗa baki, har ila yau bayan salloli na farilla lokuta ne na karɓar addu’a. Da kuma lokacin da ake ruwan sama. 


5. Ana son duk sanda za a fara addu’a a fara da godiya da yabo ga Allah Mabuwayi da Daukaka.


6. Mutum ya samu siƙƙar cewa za a biya masa buƙata, kada ya kasance mutum na addu’a amma yana kokonton cewa kamar ba za a biya masa bukata ba.


7. Rashin gaggawa ba a son bayan ka yi addu’a ka ƙosa akan cewa baka samu biyan buƙata ba. Idan ka yi addu’a ka yi haƙuri ka sani cewa Allah zai biya maka buƙata a lokacin da ya dace. Kuma ya fika sani abin da yake shi ne maslaha a gare ka.


8. Ana son a lokacin da Muke addu’a mu rinƙa zubar da waye da kuka na tsoron Allah cikin ƙanƙan da kai da tawali’u ga Allah Madaukakin Sarki.


9. Yin addu’a lokacin yalwa ba wai sai mutum yana cikin tsanani ko damuwa yake addu’a ba. Ana son a kosayaushe ka rinƙa addu’a.  


10. Azumi. Addu’ar wanda yake da azumi a bakinsa abin karɓa ce. Shi yasa ake son idan kana son kayi addu’a akan wata buƙata ta musamman ka yi azumi sai ka gabatar da addu’a.


11.Naciya: ana son idan kana da buƙata mai muhimmancin ka nace da addu’a har sai kai ga biyan bukata. Ba wai daga yin addu’a sau daya sau biyu sai ka bari ba.

12. Yi wa wasu addu'a yana da muhimmanci ka sanya Muminai da iyayen da Maƙwafta a cikin addu'o'inka.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post