MUHIMMANCI NEMAN MAGANI

Muhimmancin magani ga musulmai da ma wadanda ba musulmai ba. Har kullum shi musulmi ya sani cewa Annabi (S) ya yi magani kuma ya yi umurni ga marasa lafiya daga cikin iyalansa da sababbansa da su yi magani a duk lokacin da rashin lafiya ya same su, an ruwaito cewa wata rana wani balarabe ya zo wurin Annabi (s.a.a.w) ya tambayeshi cewa shin za mu iya yin magani idan wani rashin lafiya ya same mu? Sai Annabi (S) yace "Na'am ya bayin Allah ku yi magani domin Allah bai taba saukar da cuta ba sai ya saukar da maganin wannan cutar", illa iya abin da aka sani shi ne wani ya san maganin wata cutar wani kuma bai sa ni ba, idan mutum bai san maganın wata cuta ba bai kamata ya yanke hukuncin wannan cutar ba ta da magani ba, sai dai ya ce shi bai san maganinta ba illa iyaka.

Ke nan idan muka lura da hadisin za mu fahimci cewa Annabi (s.a.a.w) na bayani ne kan cewa duk wata cuta da muka gani tana da magani.An ruwaito cewa Abu-Huzaima ya ce "Na ce wa Annabi (S) muna yin rukiyya muna shan magani kuma muna yin riga kafi, shin waɗannan za su yi maganin abin da Allah ya ƙaddara? Sai Annabi (S) ya amsa masa da cewa "ai yin magani ma ƙaddara ce domin idan Allah (T) ya ƙaddara

mara lafiya da waraka sai ya sha magani", saboda Allah (T) gwani ne akan al'amurraSa bisa yadda ya tsara su, ta yiwu wani ya ce ai ciwo ƙaddara ce ta Allah, kuma ƙaddara Allah ba a tunkudeta, sai mu ce kamar yadda cuta take ƙaddara haka magani yake ƙaddara idan Allah (T) ya ƙaddare ka da rashin lafiya sai ya ƙaddara maka shan magani domin ka samu sauki ko waraka daga wannan rashin laitiyar kamar yadda cin abinci ke zama ƙaddarar magance yunwa tun da yunwa da koshi duk ƙaddara ce ta Allah (T).

An sami bayani daga banu Israila ce wa wata rana Annabi Ibrahim (A.S) ya ce ya Ubangiji wa ke saukar da cuta Allah (T) ya ce

masa "Ni ne", ya sake tambaya yace, wa ke ba da magani Alah (T) ya ce "Ni ne'', Annabi lbrahim yace mene ne amfanin likita? Allah (T) ya ce matum ne da na aiko da magani ta hunnunsa". Ta la'akari da wadan nan bayanan za mu fahimci cewa kowace cuta tana da magani kuma Allah ne mai warkarwa, don haka mu nemi magani a duk lokacin da muka kamu da wata cuta. Duk da cewa cutuka sun kasu kashi biyu wato da ta gangan jiki da kuma ta ruhi. Amma mu za mu takaita bayani kan cutukan gangan jiki.

1 Comments

  1. Sultan Casino | Shootercasino
    Situs Slot Online Indonesia. Situs Agen Slot Terpercaya di worrione Indonesia. Daftar Judi Online 제왕카지노 Pkv Games. Live Casino Gacor Deposit. 카지노 Slot Online Terbaik.

    ReplyDelete
Post a Comment
Previous Post Next Post